WANDA YAKAWO SALULA(WARHANU),DUNIYA
ZUWAN SALULA DUNIYA[WAYAR HANU]
DAGA MUTARIIBRAHIFASAHA
Wani masanin kimiyya da fasaha mai suna John Taylor a shekarar alif 1884 ya kirkiro na'uran tarho, wanda aka fi sani da suna telephone. Lafazin kalmar telephone ya samo asali ne daga yaren Greek wato girkawa, sannan kalmar shi telephone yana dauke ne da kalmomi guda biyu, wato tele da kuma phone. Idan aka ce "tele" a yaren girka ana nufin daga nesa, shi kuwa kalmar phone ya samo asali ne daga kalmar phonie wanda shima asalinsa daga wannan yare na greek ne, inda ya ke nufi murya. Dubi tarihin kimiyyar na'uran fanka
Kalmar telephone yana nufin murya da nesa idan ka fassara kalmar haka zai baka. A lokacin da aka kirkiro na'urar tarho anyi amfani ne da zaren igiya tare da wani abu kamar abin busa na sarewa, wanda idan mutum yayi magana a lokacin shi wannan igiyar zai girgiza kadan ta yadda shima wancan mai sauraren igiyar zai girgiza masa tayadda shima abin sarewar yana kunnensa don haka girgizan da igiyar yayi to shi zai sa abin sarewar ya fitar da sautin muryan dan adam. Wannan kimiyyar ana kiran shi da suna mechanical wave a turance.
A shekarar 1876 wani masanin kimiyyar latironiks dan kasar Scotland mai suna Alexander Graham ya kirkiro na'uran tarho mai amfani da lantarki wanda take fitar da sautin muryam mutum a karo na farko. A wancan locakin duniya tayi sambarka da wannan fasaha. Amma sai dai shi wannan tarho bayada abin danna wa wajen neman wanda za'a kira. Sai a shekarar 1970 aka kirkiro telephone wanda yake da wajen murdawa wanda shike matsayin wajen zaben wanda za'akira. Shi wannan abin murdawan ana kiranshi da suna rotary dialer a turance.Amma a lokacin wadannan tarho suna amfani ne da waya wanda ke kai sako na sabis. Akanyi magana ne tsakanin mutumin da kuke zaune gida daya ko kuma makota da juna. Sannan ba dama ka dauki tarho din ka fita da ita waje sabo da girmanta da kuma nauyinta. Dubi tarihin na'uran adana sanyi (refrigerator)
A shekarar 1973, aka kirkiro tarho wanda ake iya rike ta aje ko ina da ita wanda ake kiranta da hausa tafi da gidanka. Sannan da turanci ana kiranta da suna handheld telephone. A shekarar 1980, wani kamfanin latironiks dake kasar Amurka ya kirkiro wayar tarho mai amfani da wajen dannawa wato mai nambobi wanda akafi sani da suna dail pads a turance. Wannan cigaba bai tsaya nan ba. Domin a dalilin cigaban da aka samu na kimiyyar ilimin rediyo,tv, da kuma koyin wuta dasu komfuta. Hakan yasa dayawa daga cikin masana kimiyar latironiks sukayi ta bada tasu gudumawa wajen inganta fasahar na'urar tarho na tafi da gidanka.
A shekarar 1991 aka sami kimiyyar sabis na wayar salula wanda ake kiranshi dasuna 2G sabis wanda a turance ana kiranshi da suna digital network wanda akara kaddamar dashi a kasar Finland. A shekarar 2000, kimiYyar wayar salula ya bazu ta yadda ankawata wayoyi suna dauke da damar tura sakon sms, mms, email, internet access, da kuma video game. A shekarar 2001, sai aka kaddamar da 3G sabis wanda wani ci gaba ne a kimiyyar wayar salula wanda yake bawa wayar salula damar kallon video a shafuka na internet da sauran wasu aikace aikace wanda wayar salula zata sami damar yin su cikin sauri.
A shekarar 2009 , aka sake kaddamar da wani sabis mai karfi wanda yafi 3G sabis wanda ana kiransa da suna 4G sabis. Shi wannan sabis na 4G yana da kyau ainin wanda ya kara kawo cigaba na wayoyin zamani. A halin da ake ciki, ansami ci gaba na kimiyyar wayoyin zamani ta yadda kana gida zaka iyayin waya da mutum kana ganinshi haka shima yana ganinka. Sannan ankirkiro wayoyin komi da ruwanka wanda suna da dumbin aikace aikace wanda zasu iyayi maka. Babu shakka anaso amaida wayar salula abar more wa na rayuwa. Sai dai ansami korafe korafe a bangarori na kasashen duniya cewa, bayyanar wayar salula yana gaba gaba wajen bata tarbiyan yara da matasa sannan ya taimaka musu wajen rashin maida hankali wajen sha'anin karatun su.
Comments
Post a Comment