TARISHIN IMAM MALIK
CIKAKKEN TARISHIN IMMAM MALIK, Cikakken sunan sa shine Abu 'Abdullah Malik ibn 'Anas ibn Malik ibn Amr al-Asbahi an haifeshi a birnin Musulunci Madina a shekara ta 93 bayan Hijirar Manzon Allah Annabi Muhammad S.a.w, dai-dai da shekara ta 714 miladiyya. Tarihin Imam Malim Bn Anas Marubuci: SADIQ TUKUR GWARZO Ance asali, tsatson sa daga ƙasar Yemen ne, daga ƙabilar al-Asbahi, amma sai kakansa Abu Amir ya dawo Madina da zama bayan ya karɓi musulunci. Mahaifinsa Anas ya ɗauki ilimi a wajen Halifa Umar bn Khattab R.A, kuma dashi akayi aikin tattarawa gami da rubuta littafin Alqurani maigirma a zamanin Halifancin Usman bn Affan R.A. A haka kuma har Allah ya ƙadarta haihuwarsa a birnin na Madina. A Littafin Muwaɗɗa nashi Imam Malik ɗin, an faɗi siffar Imam Malik a matsayin dogo kakkaura, mai cikakken farin gemanya da korayen idanuwa. Imam Malik ya zamo babban masani a Madina, ko ace a duk duniyar musulunci ma baki ɗaya. Anan madina yayi karatunsa, ya kuma karɓi ilimin sa ne daga han...