Posts

HAUSA KAFIN RUBUTUN BOKO

  Hausa kafin Rubutun Boko   Kafin karni na sha tara, kuma kafin zuwan turawan mulkin mallaka kasar hausa, ɗaukacin masana sun haɗu akan cewa babu rubutun AaBaCaDa (da akafi sani da boko) a kasar hausa, rubutun larabci da kuma hausa da larabci (Ajami) kaɗai aka sani.    Shi kansa rubutun na Ajami, dattijo Marigayi Alh Muhammad Koki wanda yana cikin mutanen da suka tallafawa turawa wajen aikin tafinta har aka samar da Gidajen tarihi na kano dana sokoto cewa yaji kaka-da-kakanni ana cewa asalin hausa babu rubutu har sai lokacin da larabawa suka zo da musulunci. A lokacin ne aka rinka amfani da rubutun larabci wajen sadarwa da kuma yin rubuce-rubuce. Har ma yace a wancan zamanin, idan kanaso ka tura wani sako ga wani ɗan uwanka dake rayuwa acan nesa dakai, sai dai kaje ka samu malami daya kware a fannin larabci, ka faɗi masa sakon shikuma yana rubutawa da alkalami a takarda, sannan ka biya lada, kai kuma ka naɗe sakon ka turawa ɗanuwan naka ta hanyar fatake. Shima ɗan u...

IN ZAKA FADI KAYI GASKIYA

Image
  Al-Amarin Kare Na Daga Cikin Abubuwan Ban Mamaki AL-AMARIN KARE NA DAGA CIKIN ABUBUWAN BAN MAMAKI Kare yana daga cikin dabbobin da Allah ya haramtawa Musulmi cin namansa. Ba shakka kare wata dabba ce da ba wata mai kima ko daraja ba ce a wajen mutane da dama, musamman Musulmi. Cikin ikonSa Subhanau Wata'ala, ya sanya fahimtar juna tsakanin Kare da Bil-Adama, babu shakka dukkan dabbobin da Allah ya hiltta babu wata dabba da ta kai kare sabo da Mutane, wannan ta sanya a kasashen Turai da Amerika ake lissafa kare a zaman daya daga cikin Iyalin gida, ko ahalin gida, kare yana samun kulawa ta musamman a wajensu. Sukan bashi wata irin daraja da ta shallake irin wadda wasu mutane suke samu a wasu sassa na duniyar nan! Allah buwayi gagara misali, shi ya sa da ya tashi bayar da labarin ASHABUL-KAHFI a cikin al-qur'ani mai tsarki, sai ya bayar da labarin har da karen da yake tare da su, wato kare ya lizimci mutanan kirki!  Shin waye kare? Wani bincike ya nuna cewar, kare ya rayu a cik...

TARISHIN LAILA DA MAJANUN

Image
  Labarin Soyayyar Laila Majnun... Nasan kun daɗe kuna jin Labaran Soyayya Amma na Tabbata baku taɓa cin karo da irin wannan ba.... Waye  majnun lailah? Wani mutumne da aka yi a daular banu umaiyya abisa zancemafi inganci. Sunansa shine "Qais Bn Mulawwah" daga "kabilar Banu Amir", Qais balaraben ƙauyene, ya taso tare da ‘yar gidan kawunsa mai suna "LAILA BNT MAHDI IBN SA’D" Amfi sanin Laila da sunan "Laila Aamiriya", tare suka taso tun suna yara suna kiwon dabobi har suka girma, suka fita daga sahun yara suka kai munzalin balagha. A Yayin da alamun nuna balaga da cikar budurci suka gama bayyana ajikin Laila sai "Qais" ya ruɗe soyayyarsa gare ta, hankalinsa ya dugunzuma ya tashi. Domin a wannan lokacin ne "Qais" ya Lura da irin kyawun dirin da Allah ya yiwa abokiyarsa "Laila", a kullum soyayyar Laila sai kara tashin gwauron zabi take yi a cikin zuciyar "Qais", a cikin wannan yanayi ne "Qais" ya shi...

TARIHIN ASALIN YAREN HAUSA

 Masana tarihi na tababa game da gaskiyar tarihin Bayajidda amma mutumin wanda ake dauka a matsayin gwarzo na ci gaba da kasancewa a tarihin Malam Bahaushe. Rayuwarsa:  Babu wani kwakkwaran bayani da ake da shi game da shekarar da aka haifi Bayajidda da ma sanda ya rasu kasancewar galibin tarihinsa da aka bayar, ta fatar baka ne. Ana tunanin cewar asalinsa mutumin Bagadaza ne a kasar Iraki kuma bayan zuwansa daular Borno ne ya koma Daura da ke jihar Katsina da zama.   Asalin tarihinsa:  Wasu na cewar Bayajidda ya bayyana ne tsakanin karni na 16 zuwa na 19 amma kuma akwai shaidar kasancewarsa a al'adar Hausawa tun cikin karni na 9 zuwa na 10.   Suna:  Ana zaton asalin sunansa Abu Zaid. An samo sunansa na Hausa da aka sanya masa wato Bayajidda daga jimlar nan ta "Ba ya ji da”, ma'ana a baya ba ya jin Hausa. 01:40 mintuna TUSHEN AFIRKA | 10.01.2018 Tarihin Bayajidda da asalin Hausa bakwai a Najeriya Macijiya:  An bayyana cewar Bayajidda ne ya kashe wata m...

TARIHIN FULANI A DUNIYA

 Tushen Fulani Fulani dai kabila ce da tarihi ke turke asalinta tun ƙarni na 15 daga wasu manyan yankuna biyu da ke kasashen Senegal da kuma Guinea Conakry, wato Futa Toro da kuma Futa Jalloh. Daga nan ne suka ci gaba da bazuwa cikin kasashen duniya musamman yammaci da kuma tsakiyar nahiyar Afirka domin nema wa dabbobinsu abinci da kuma ingantacciyar rayuwa. Ko da yake babu tsayayyen adadi na yawan Fulani a duniya, amma kiyasi na nuna yawansu ya kai akalla miliyan 45, kuma sun fi yawa ne a kasashen yammacin nahiyar Afirka. Dakta Ahmad Shehu masanin tarihin Fulani kuma malami a sashen nazarin harsuna da ke Jami'ar Bayero ta Kano ya ce, "baya ga yammacin Afirka, Fulani na nan a kasashe da dama na nahiyar musamman tsakiyarta". Kasashen Fulani Wata dabi'a da aka san Fulani da ita ita ce yawo da dabbobi daga wata kasa zuwa wata, kuma wannan ne dalilin da ya sa ake samun su a kasashe da dama musamman a nahiyar Afirka. Nigeria@60: Waiwaye kan tarihin Yarbawa bayan shekara 60...

TARISHIN SHEIKH USMAN DAN FODIO

Tarihin Daular Usumaniyya ba za ta cika ba matukar ba tabo tarihin Mujaddadi Shehu Usman Fodiyo ba. Saboda haka ga takai taccen tahirinsa nan kamar haka: An haifi shehu usman dan fodiyo a ranar lahadi karshen watan safar, shekarar hijra ta 1168 wanda ya zo daidai da (December 1754) a wani kauye mai suna Maratta. Daga baya iyayensa suka tashi zuwa Degel a kasar Gobir. A yau babu wannan gari na Gobir kodayake an yi shi ne kusa da sabon birni a jihar sokoto, iyaka da kasar Nijar. A halin yanzu kauyen da aka haifi shehu yana cikin kasar Nijar. Shehu ya yi wayo da bude idonsa a cikin gidansu, a kuma kauyensu wato Degel. Mahaifinsa Muhammadu Fodiyo, shi ne ya rada masa suna Usman (wato sunan kakansa kenan). Muhammadu Fodiyo. Wanda Fodiyo a harshen Fulatanci na nufin Faqihi masanin Fiqihu. Nasabar Shehu shi ne dan Usman dan Salihu dan Ayuba dan Haruna dan Muhammad gwandu dan Jubo dan Muhammadu Sambo dan Ayuba dan Masirana dan Baba dan Musa Jakullo. Musa Jakullo shi ne wanda ya yi hijra da mut...